BlinkSync

Yadda kadojin Wukari ma su tarihi ke zaman lafiya da jama'a

- Al'ummar Wukari sunyi hijira taso ne daga Yemen misalin shekaru 1000 da suka shude inda suka yada zango a Wukari wanda ke jihar Yobe a yanzu

- Sun kasance masu riko da addinan gargajiya ne wannan lokacin wanda ya hada da bori da kuma bautan wasu kadoji 5 da aka ce suna kare garin daga masifu

- Kadojin sukan kai gaisuwa fadan sarkin garin duk Juma'a a zamanin magabata kuma ance ba su taba kashe mutum ko dabba ba

- Kadojin 5 masu mabanbanta launuka na zaune ne a wata kududufi wadda ruwan ta ke warkar da cututuka kuma akan nemi taimakonsu a duk lokacin da wata bala'i da bulla a garin

Kamar yadda tarihi ya nuna, Kadojin garin Wukari sun kasance abin girmamawa da daraja ga 'yan kabilan jukun wanda asalinsu daga masarautar Kwararafa su kayi hijira zuwa garin Wukari da ke Jihar Yobe misalin shekaru 400 du suka gabata.

Kadojin guda biyar masu launuka daban-daban sune zaune ne a wata kududufi dake Kudancin fadar Aku-Uka a garin na Wukari mai dimbin tarihi.

Basaraken garin Wukari (Kinda Acio na Wukari) Mr. Manu Danladi Boushe wanda ya zaga da wakilin Daily Trust zuwa kududufin tare da masu yiwa kududufin hidima ya ce an kafa garin ne misalin shekaru 400 da suka wuce.

DUBA WANNAN: Masifar da ta fi Boko Haram na nan tafe a kasar nan - Sarki Sanusi

Ya ce mutanen Kwararafa sun fara hijira ne shekarar 360AD yayin da suka baro Yemen zuwa Masar sannan daga nan suka nufi Ngazargamu da ke jihar Yobe kusan shekaru 1000 da suka shude. Kinda Acio ya ce daga Ngazargamu mutanen Kwararafa sunyi hijira zuwa Wukari mai nisan kilomita 74 yammacin garin.

Inda suka yada zango shine suka saka wa suna Kwararafa kuma yana kusa da hanyar Jalingo-Wukari da ke karamar hukumar Gassol a jihar Taraba.

Mr. Manu yayi bayanin cewa al'adar 'yan kabilan Jukun ne tuntubar bokaye da 'yan tsibu wanda ke fadawa Sarakunan Jukun abinda ka iya faruwa tun kafin ya afku.

"Magabatan mu suna da wata dabi'a na tuntubar masu duba idan za ayi tafiya, yaki ko ran gadi tun kafin su baro Yemen kuma har yanzu ba ayi watsi da wannan dabi'ar ba. Bayan tuntubar magabatan mu ne muka yi hijira zuwa Kwararafa," inji shi.

Ya ce akwai kadoji guda 5 cikin kududufin masu launuka daban-daban kuma kowannen su yana da kogon da ya ke zaune wadda ta hade da Rafin Benue da Donga da Katsina Ala. A cewarsa idan rani ya zo kadojin na sulalewa zuwa rafin amma da damina sai su dawo kududufin.

Ya ce kadojin sun da yawo cikin garin Wukari ba tare da sun taba kowa ba har sukan tafi gaisuwa a fadar Aku-Uka a duk ranar Juma'a a zamanin magabata. Ya kuma ce kadojin na da baiwa na musamman kuma duk wanda ya yi niyyar taba su zai hadu da bala'i wasu har mutuwa ma su kayi.

"Kadojin suna zaune lafiya da mutanen gari. Ba su kashe dabobi ko mutane. Ba mu taba samun labarin cewa kadojin sun kashe daba ko mutum ba," inji Kinda Acio.

Sai dai ya ce a yanzu sun dena zuwa fadar Aku-Uka domin gaisuwa amma suna yawonsu cikin gari ba tare da wata matsala ba.

Binciken da majiyar Legit.ng Hausa tayi ya nuna cewa akwai wasu maguzawa daga Zaria ko Katsina da suka hade da mutanen Jukun inda suke bautan kadojin tare tun a lokacin da suka iso Kwararafa.

Su kan kashe dabobi domin bawa kadojin a duk shekara yayin wata buki da ake kira Bori da Gani a da akeyi a gaban kududufin.

Daga wannan lokacin ne kabilun biyu suka zama masu kula da kududufin. A kan tuntubi masu kula da kududufin kafin a gudanar da buki ko kuma neman magani ko waraka daga kadojin a duk lokacin da bukatan hakan ya taso.

Malam Usman ya shaidawa majiyar Legi.ng Hausa cewa ya gaji hidimar kududufin ne daga iyaye da kakaninsa kuma aikinsa shine gabatar da dabobi ga kadojin a lokacin buki ko kuma wata bukata ta taso.

A cewarsa, duk lokacin da wani musifa ko bala'i ya samu mutanen garin, su kan taru gaban kududufin sannan a yanka baka sa kuma a jefa naman a cikin kududufin domin rokon kadojin su kawo sauki a al'ummar garin.

Ya kuma ce ba a kamun kifi a kududufin domin duk kifin da aka kama ba zai dahu ba ko da kuwa an yini ana dafa shi a cikin tukunya ne.

"Ruwan kududufin yana maganin cututuka daban-daban kuma mutanen Jukun daga ko ina a duniya sukan dawo gida su nemi ruwan kududufin domin samun waraka daga duk wata cuta da ke damunsu," inji shi.

Ya ce a halin yanzu, mutane ba su cika damuwa da bikin na Bori da Gani ba a garin na Wukari saboda zuwan addinan musulunci da kiristanci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHB9kWlrbXFnYsaisMOaZKSZlKS3qrqMsKykmaKeeq6tjKysZqyRp7aptYyknGaykaKur3nLmp2isZFisaJ5yZqkmplencGuuA%3D%3D

Martina Birk

Update: 2024-08-08