Naira Ta Yunuro, Ta Yi Raga Raga da Dalar Amurka a Kasuwar Canji Ta Najeriya
- Naira ta farfaɗo kan Dalar Amurka bayan kwanaki biyu tana shan ƙasa a kasuwar hada-hadar musaya ta gwamnati a Najeriya
- Farashin canjin ya dawo N1,564.48 kan kowace Dalar Amurka ranar Alhamis, 15 ga watan Agusta daga N1,586/1$ a ranar Laraba
- Masana sun yi hasashen cewa Naira za ta ci gaba da tasowa saboda wasu sababbin matakai da babban banki CBN ya ɗauka
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Darajar kuɗin gida Najeriya watau Naira ta ƙara tashi kan Dalar Amurka a kasuwar canji ta gwamnati a ranar Alhamis, 15 ga watan Agusta, 2024.
Ƙimar Naira ta farfaɗo zuwa N1,564.48 kan kowace Dala guda a jiya Alhamis idan aka kwatanta da N1,586/1$ na ranar Laraba, 14 ga watan Agusta, 2024.
'Yan bindigar da suka sace ɗaliban jami'o'i 2 a Arewa sun turo saƙo, sun faɗi buƙatarsu
Kuɗin Najeriya sun yi wannan farfaɗowa ne bayan faɗuwar da Naira ta yi na kwanaki biyu a jere duk da babban banki CBN ya ɗauki wasu matakai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane matakai CBN ke ɗauka?
Babban bankin Najeriya (CBN) ya sayar da Dala ga bankuna 26 ranar Laraba, 7 ga watan Agusta, sannan kuma ya kara ware masu karin Daloli ranar Jumu'a.
CBN ya ce yana amfani da tsarin rDAS wajen cinikayyar kuɗin ketare ne domin rage bukatar Daloli, wanda ya yi imanin cewa ya na matuƙar cutar da kudin Najeriya.
Masana harkokin kudi sun bayyana cewa wannan yunƙuri na CBN ya sa ƙimar Naira ta fara dawowa a kasuwar hada-hadar kuɗi.
Naira ta kara daraja kan Dala
A rahoton ƙasuwar FDMX da ta wallafa a shafinta, farashin sayen kowace Dala a jiya Alhamis ya fara ne daga N1,515 mafi karanci, sannan ba ya haura N1,600/1$.
'Yan bindiga sun sace kwamishina da matarsa a hanyar zuwa ɗaura auren ɗiyar gwamna
Adadin kudin kasashen ƙetare da aka yi ciniki sun ƙaru zuwa $149.25m daga $92.39m da aka yi kasuwancinsu ranar Laraba, 14 ga Agusta, 2024.
Kotu ta ƙwace kuɗi daga hannun Emefiele
A wani rahoton kuma kotu ta umurci tsohon gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele da ya janye ikon mallakar $2,045,000 da aka alakanta su da shi
Akintayo Aluko na babbar kotun tarayya ne ya bayar da wannan umarni, inda ya kara da cewa ana zargin kudaden na haram ne.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGlmZYV3hZNmpZqhopZ6ta2MsqBmqpGcrm6%2BwKCYZpyRYrGiuMCrZJqlpae4onnYmrCipl2Zrm6vwadkspldma62t8hmqpqakZevqnnMmquao5GefA%3D%3D